rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Spain Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ronaldo na son barin Spain saboda haraji

media
Cristiano Ronaldo na Real Madrid REUTERS/Rafael Marchante

Cristiano Ronaldo ya ce zai bar Real Madrid saboda baya son sake buga wasa a Spain sakamakon zarginsa da kaucewa biyan haraji kamar yadda wata jaridar a kasar Portugal ta ruwaito.


Ronaldo ya shaidawa Real Madrid cewa yana son barin kungiyar kamar yadda kafar A Bola ta sunsuno daga wata majiya kusa da dan wasan.

Ana zargin Ronaldo da kaucewa biyan harajin kudi kusan fam miliyan 15, zargin gwarzon dan wasan na duniya ya musanta.

Masu gabatar da kara na zargin Ronaldo da amfani da wani kamfanin kasashen waje domin kaucewa biyan haraji a gwamnatin Spain.

A watan Nuwamban da ya gabata ne Ronaldo ya sanya hannu kan sabuwar kwangilar shekaru 5 inda zai ci gaba da murza leda a Madrid har zuwa 2021.

Messi ma ya fuskanci shari’a inda aka yanke masa hukuncin dauri a gidan da za a iya dakatarwa saboda kaucewa biyan haraji a Spain.