Isa ga babban shafi
Wasanni-Tennis

An fitar da Murray daga gasar Aegon a zagayen farko

An fitar da Andy Murray daga gasar wasan kwallon Tennis ta Aegon da ke Gudana a Birmingham tun a zagayen farko, wanda kuma shi ke rike da kofin gasar.

Mai rike da kofin gasar Aegon Andy Murray wanda Jordan Thompson ya fitar a zagayen farko.
Mai rike da kofin gasar Aegon Andy Murray wanda Jordan Thompson ya fitar a zagayen farko. eurosport
Talla

Wani abin mamaki da masharhanta ke cigaba da muharawa a kai shi ne, ganin cewa wanda ya samu nasarar yin waje da Murray, wato Jordan Thompson, yana a matsayi na 90 ne, a matakin kwarewa, tsakanin jerin ‘yan wasan kwallon Tennis a duniya.

Thompson, dan kasar Australia, ya samu nasara kan Murray da 7-6 7-4 da kuma 6-2.

Karo na farko kenan da Murray dan kasar Birtaniya ya yi rashin nasara a zagayen farko na irin wannan gasa, tun bayan shekara ta 2012.

Idan ba’a manta ba, jiya a dai gasar ta Aegon ‘Yar wasan kwallon Tennis, Naomi Broady ‘yar Birtaniya, kuma ta 111 a matakin kwarewar wasan na tennis, ta doke Alize Cornet ‘yar kasar Faransa, ta 38 a duniya da 7-6, 7-3 da kuma 6-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.