Isa ga babban shafi
Wasanni-Ingila

Iheanacho zai zauna a City duk da fuskantar kalubale

Bisa dukkanin alamu dan wasan gaba na kungiyar Manchester City daga Najeriya Kelechi Ihenacho, zai ci gaba da zama a kungiyarsa ta City, duk da babban kalubalen da yake fuskanta na dumama benci a kungiyar.

Kelechi Iheanacho na kungiyar Manchester City.
Kelechi Iheanacho na kungiyar Manchester City. OLI SCARFF / AFP
Talla

Tun bayan zuwan Gabriel Jesus dan kasar Brazil, a kakar wasan bara, Ihenacho ya fara zaman dabaro a bencin Manchester City, saboda karkata wajen shi fiye da Ihenachon da mai horarwa Pep Guardiola yayi.

A kakar wasan Premier da ta gabata, an fara wasanni biyar ne kawai da Iheanacho mai shekaru 20, daga cikin wasanni 20 da ya bugawa City, wanda kuma ya samu zura kwallaye 4 kawai.

Hakan yasa kungiyoyin West Ham, Everton, Swansea City, Leicester City, da kuma Crystal Palace suka bayyana sha’awarsu sayan Iheanacho.

Sai dai wata majiya daga iyalansa, ta tabbatar da cewa zancan barinsa City bai ma taso ba, kasancewar babu daya daga cikin kungiyoyin da ke masa tayi, da zata iya biyansa albashin Fan dubu 85 da yake dafewa a duk mako guda, a kungiyarsa ta Manchester City.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.