Isa ga babban shafi
Rasha

Jamus da Chile za su buga wasan karshe a gasar zakarun Nahiyoyi

Kasar Jamus da Chile za su buga wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Nahiyoyi da ake gudanarwa a kasar Rasha bayan Jamus a jiya Alhamis ta ba Mexico kashi ci 4 da 1 a wasan kusa da karshe.

Jamus ta lallasa Mexico 4-1 a wasan dab da karshe a Rasha
Jamus ta lallasa Mexico 4-1 a wasan dab da karshe a Rasha REUTERS
Talla

A ranar lahadi ne za a yi fafatawar karshe domin fitar da zakara tsakanin Jamus da ta lashe kofin duniya da kuma Chile da lashe kofin gasar kasashen kudancin Amurka.

Jamus da Chile sun hadu a zagayen farko a gasar inda suka tashi 1 da 1

Kafin a buga wasan karshen za a yi karawar neman na uku tsakanin Portugal da Mexico.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.