rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

League 1 Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dani Alves ya koma PSG

media
Paris Saint-Germain ta gabatar da Dani Alves Reuters

Paris Saint Germain ta gabatar da Dani Alves dan wasan Brazil da ta karbo daga Juventus inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu da kungiyar.


Dan wasan ya ce yana fatar kafa tarihi idan ya lashe kofin zakarun Turai da Paris Saint Germaine.

An yi zaton dan wasan zai koma Manchester City City domin sake haduwa da tsohon kocinsa Pep Guardiola da ya horar da shi a Barcelona.

Amma Alves ya yi watsi da bukatar bayan PSG ta taya shi fiye da kudaden da City ta ce zata bashi.

Dan wasan zai karbi kudi euro miliyan 14 a duk shekara.