rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Olympic Wasanni Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Olympics: Los Angeles zai karbi bakuncin wasannin 2028

media
Magajin garin Los Angeles, Eric Garcetti REUTERS/Mike Blake

Birnin Los Angeles ya bayyana kudirin neman karbar bakuncin wasannin Olympics a shekarar 2028, a wani mataki da zai ba birnin Paris damar karbar bakuncin wasannin a 2024.


Paris da Los Angeles na fafatawa ne da juna kan neman karbar bakuncin wasannin Olympics a 2024 bayan kammala wasannin a 2020 da za a gudanar a Tokyo.

Yanzu birnin Los Angelses ya sauya ra’ayi daga 2024 zuwa 2028.

A ranar 13 ga watan Satumba ne hukumar wasannin Olympic za ta sanar da biranen da suka yi nasara.

Paris na son karbar bakuncin wasannin a 2024 domin ya yi daidai da shekaru 100 cur da birnin ya taba karbar bakuncin wasannin a 1924.