Isa ga babban shafi
Spain

Ronaldo ya musanta kaucewa biyan haraji

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya musanta zargin ya kaucewa biyan haraji a Spain bayan ya gurfana a kotu a jiya Litinin.

Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo na kungiyar Real Madrid
Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo na kungiyar Real Madrid REUTERS/Rafael Marchante
Talla

Ronaldo ya shaidawa kotun Spain cewa bai taba kaucewa biyan haraji ba kuma ba zai taba yi ba.

Zakaran gwarzon dan wasan na duniya ya ce a kullum yakan bibiyi lamurransa domin tabbatar da ya biya haraji daga kudaden ya ke samu saboda baya son shiga matsala.

Ana zargin Ronaldo ne da kaucewa biyan harajin kudi kusan miliyan 15 na yuro a tsakanin 2011 zuwa 2014.

Za a dai iya cin Ronaldo tarar kudi kusan miliyan 28 na euro idan har kotu ta kama shi da laifi tare da yanke ma sa hukuncin daurin kusan shekaru 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.