Isa ga babban shafi
Wasanni-Qatar

Gasar cin kofin Duniya: Qatar na kashe dala miliyan 500 duk mako

Shugaban shirye-shiryen da kasar Qatar ke yi domin karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta Duniya a shekara ta 2022, Hassan Al-Thawadi, ya musanta cewa takkadama tsakaninsu da wasu kasashen Larabawa ya tsayar da shirye-shiryen da ta ke yi, biyo bayan rufe iyakokin da Saudiya ta yi da kasar ta Qatar.

Gwamnan babban bankin kasar Qatar Sheikh Abdullah bin Saoud al-Thani
Gwamnan babban bankin kasar Qatar Sheikh Abdullah bin Saoud al-Thani REUTERS/Hamad I Mohammed/File Photo
Talla

A cewar Hassan, tasirin da wannan koma bayan Diflomasiyyar bai taka kara aya karya ba, kan shrin da suke na karbar bakuncin na gasar kwallon kafar ta duniya

Qatar dai na kashe jimillar kudi dala miliyan 500 a duk mako guda, kan shirin da ta ke na karabar bakuncin gasar.

A ranar biyar ga watan Yunin da ya gabata ne kasashen Saudiya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da kuma Masar suka yanke hulda da Qatar, bisa zarginta da goyon bayan ayyukan ta’addanci, ta hanyar tallafawa kungiyoyin da aka bayyana su a matsayin na ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.