rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kwallon Kwando Najeriya Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya ta lashe gasar kwallon kwando ta nahiyar Africa

media
Tawagar 'yan wasan kwallon kwando ta Najeriya D'Tigress da ta lashe kofin gasar ta nahiyar Afrika a Bamako, Mali. Punch

Tawagar kwallon Kwando ajin mata da ke wakiltar Najeriya, wato D’Tigress, ta samu nasarar lashe kofin gasar kwallon Kwando ta nahiyar Africa, karo na uku, da ta gudana a babban birnin Mali, Bamako.


Najeriya ta samu nasarar ce bayan lallasa kasar Senegal da kwallaye 65 da kuma 48 a wasan karshen da suka fafata a jiya Lahadi.

Ko wasan rukuninsu na B da suka fafata a farkon wannan gasa, ‘yan matan kwallon kwandon na Najeriya, sun lallasa tawagar Senegal da kwallaye 58 da kuma 54.

Ba dai a wannan karon bane kadai Najeriya ke doke Senegal a wasan karshen na cin kofin kwallon kwandon nahiyar Afrika ajin mata, domin a shekara ta 2005 D’ Tigress din sun lallasa Lionesses din na Senegal da kwallaye 64 da kuma 57 a garin Abuja.

Yanzu haka dai Najeriya na da kofunan wannan gasa har uku, shekara ta 2003, 2005, da kuma wannan ta 2017.