Isa ga babban shafi
Wasanni

An kusa kai wa Mbappe hari a wasansu da Celtic

Wani mai goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Celtic, ya afka cikin filin wasa da zimmar kai hari kan dan wasan PSG Kylian Mbappe a yayin fafatawar da kungiyoyin biyu suka yi a jiya Talata a gasar zakarun kungiyoyin Turai.

Kylian Mbappé na PSG
Kylian Mbappé na PSG REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Lamarin ya faru ne a lokacin hutun rabin lokaci a filin wasa na Celtic Park, wato jim kadan kenan da kwallo ta uku td PSG ta zura a ragar Celtic.

Celtic wadda ta karbi bakwancin PSG, za ta fuskanci hukunci daga hukumar kwallon kafar nahiyar Turai.

Kocin Celtic, Brenden Rodgers, ya ce, kungiyar za ta hukunta wannan mutumin da ya aikata wannan laifi na kokarin kai hari kan Mbappe da ya zura kwallo ta uku a fafatawar da suka yi nasara da ci 5-0.

A karon farko kenan da Celtic da ta kasance zakara a Scotland, ke shan mummunan kashi a gida a wata gasa a nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.