rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dan Birtaniya ya zagaya duniya cikin kwanaki 78

media
Mark Beaumont da ya kafa tarihin zagaya duniya cikin kasa da kwanaki 80. AFP

Mark Beaumont dan kasar Birtaniya, ya kafa tarihin zama na farko da ya zagaya duniya cikin kwanaki 78, awanni 14 da kuma mintuna 14.


Beaumont mai shekaru 34, ya kawo karshen tarihin da aka taba kafawa na zagaye duniya a kan babur cikin kawanaki 23.

Cikin kwanaki 76 da ya kwashe yana tafiyar Beamont yayi tafiyar sama da awanni 16, inda ya shafe kilomita 29,000 a kan Keken.

Beaumont ya fara tafiyar ce daga birnin Paris, a ranar 2 ga watan Yuln da ya gabata, daga nan sai ketara nahiyar turai zuwa kasar Rasha, da Mongolia, daga bisani ya isa birnin Beijing.

Daga Beijing ne ya shiga jirgin sama zuwa garin Perth dake yammacin kasar Australia, bayan saukarsa yayi mafani da Keken ketarawa zuwa kasar New Zealand, daga nan kuma ya sake shiga jirgi zuwa jihar Alaska ta Amurka.

Mark Beaumont ya karkare ziyarar tasa ce a kasar Canada, daga nan ya hau jirgin sama zuwa birnin Lisbon na Portugal.