Isa ga babban shafi
wasanni

Dembele na Barcelona zai yi jinyar watanni uku

Tsadadden dan wasan Barcelona, Ousmane Dembele zai yi zaman jinyar watanni uku da rabi bayan an yi ma sa tiyata a yau Talata.

Ousmane Dembélé na Barcelona
Ousmane Dembélé na Barcelona REUTERS/Albert Gea
Talla

Dembele da Barcelona ta siya a kan Euro miliyan 105 daga Borussia Dortmund ya samu raunin ne a kafarsa a lokacin da ya ke buga wa kungiyar wasan farko a gasar La Liga a ranar Asabar da ta gabata, in da ta samu nasara akan Getafe da ci 2-1.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau, Barcelona ta ce, an kammala yi wa dan wasan tiyata a birnin Helsinki a kafarsa ta hagu.

Yanzu haka dai, dan wasan ba zai buga sauran wasannin da Barelona za ta yi a matakin rukuni a gasar zakarun kungiyoyin nahiyar Turai ba.

A karon farko kenan da Dembele ke samun mummunan rauni tun bayan da ya shahara a fagen kwallon kafa a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.