Isa ga babban shafi
Wasanni

Dole Tevez ya rage taiba ko mu sallame shi - Wu Jingui

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua dake China, Wu Xiaoh ya ce dan wasansu na Gaba Carlos Tevez ya gaza bugawa kungiyar wasa yadda ya kamata, a dai dai lokacin da kungiyar ta Shenghai Shenhua ke daf da fadawa ajin ‘yan dagaji.

Carlos Tevez na kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua, yayin fafatawa da kungiyar Brisbane Roar, a birnin Shanghai na China..
Carlos Tevez na kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua, yayin fafatawa da kungiyar Brisbane Roar, a birnin Shanghai na China.. REUTERS/Stringer
Talla

Tevez wanda tsohon dan wasan Manchester United da Juventus ne kafin komawa China, yana fuskantar suka daga daraktoci da kuma magoya bayan kungiyarsa da Shenghai, duba da cewa a kowane mako guda yana dafe albashin Fan dubu 615,000 a matsayin albashi, ba kuma tare da yana tabukawa kungiyar komai ba.

A halin yanzu kocin kungiyar ta Shenghua Wu Jingui ya gargadi Tevez da cewa mataki na farko ma tilas ne a rage taiba, domin a cewar Jingui hauhawa kamar farashi da Teves ke yi, yana taka rawa wajen gaza ciwa kungiyar kwallaye.

Tun bayan bude kakar wasa ta bana kwallaye uku kawai Tevez ya kankarowa Shenghai Shenhua, kwallo daya tilo kuma ta karshe ita ce wadda ya jefa a wasan da Shanghai SIPG ta lallasa su da kwallaye 6-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.