rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Cavani yayi watsi da tayin bashi alawus na euro miliyan 1

media
Edison Cavani, yayinda ya gaza jefa kwallo a ragar kungiyar Lyon, bayan samun damar bugun daga kai sai mai tsaron gida. REUTERS/Benoit Tessier

Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain ta yi wa dan wasanta na gaba Edison Cavani tayin rika biyanshi euro miliyan daya a matsayin alawus na musamman, domin lallashinsa ya rika bai wa Neymar damar bugun daga kai sai mai tsaron gida.


A makon daya gabata ne aka samu sa’insa tsakanin Neymar da Cavani, bisa wanda ya dace yayi bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da suka samu nasara kan Lyon da kwallye 2-0, a waccan lokacin dai duk da bukatar amfani da damar bugun da Neymar ya nuna, Cavanin ne ya buga kuma ya gaza jefa kwallon a raga.

A wani yunkurin kawo karshen takaddamar ce, shugaban kungiyar ta PSG Nasser Al-Khelaifi ya yi wa Cavani tayin rika biyanshi alawus na euro miliyan daya, sai dai Cavani yaki amincewa da hakan.

A jimlace, tun daga kakar wasa ta 2013 zuwa yanzu, Cavani ya ciwa kungiyarsa ta PSG kwallaye 95 a wasanni 140 da ya buga.