Isa ga babban shafi
Bundesliga

Bayern Munich ta sallami Ancelotti

Bayern Munich ta kori kocinta Carlo Ancelloti bayan kungiyar ta sha kasha ci 3-0 a paris gidan Paris Saint-Germain a gasar zakarun Turai .

Bayern Munich ta kori Carlo Ancelotti bayan ta sha kashi ci  3-0 a gidan Paris Saint-Germain.
Bayern Munich ta kori Carlo Ancelotti bayan ta sha kashi ci 3-0 a gidan Paris Saint-Germain. Reuters/Wolfgang Rattay
Talla

Kungiyar ta sanar da sallamar Ancelotti ne a yau Alhamis kamar yadda ta wallafa a shafinta na intanet.

Mataimakinsa ne Willy Sagnol Bafaranshe aka ba aikin horar da Bayern Munich na rikon kwarya bayan ta raba gari da Ancelotti.

Tun kafin wasan jiya da PSG, Ancelotti ke fuskantar barazana da kalubale musamman salonsa na zubin ‘yan wasa.

Ya sha suka kan yadda ya ajiye manyan zaratan Bayern Munich a benci Franck Ribery da Arjen Robben da Mats Hummels.

Bayern dai yanzu na matsayi na uku a teburin Bundesliga, tazarar maki uku tsakaninta da Dortmund. Yayin da a ranar lahadi za ta kai wa Hertha Berlin ziyara.

Ancelotti dai kwararren koci ne wanda a tarihi ya jagoranci manyan kulubluka da suka hada da Juventus da AC Milan da Chelsea da PSG da Real Madrid.

Kuma kofi uku yana lashewa na gasar zakarun Turai.

A kakar da ta gabata, kakarsa ta farko a Munich ya taimakawa Bayern Munich lashe kofin Bundesliga karo na 5 a a jere bayan ya gaji Guardiola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.