Isa ga babban shafi
wasanni

Barelona ta yi wasa a bayan fage saboda rikicin Catalonia

Kungiyar Kwallon Kafa ta Barcelona ta yi wasanta da Las Palmas a bayen fage bayan hukumomin gasar La Liga sun ki amince wa da bukatar Barcelona ta dage wasan wanda a aka yi shi a rana guda da aka gudanar da zaben raba gardama game da ballewar yankin Catalonia daga Spain.

Filin wasa na Camp Nou mai daukan mutane dubu 99
Filin wasa na Camp Nou mai daukan mutane dubu 99 REUTERS/Albert Gea
Talla

Barcelona ta soki yadda jami’an tsaron Spain suka keta hakkin jama’ar yankin Catalonia da ta ce, sun fito ne don neman ‘yancinsu amma aka raunata da dama daga cikinsu.

A dalilin haka ne, Barcelona ta yi wasan a bayan fage a filinta na Camp Nou mai daukan mutane dubu 99.

Barcelon ta dauki wannan matakin ne don nuna bacin ranta kan yadda ‘yan sanda suka ci zarafin jama’a kamar yadda shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu ya bayyana.

Dubban magoya bayanta sun yi cincirindo a wajen filin Camp Nou ba tare da sun samu damar shiga filin wasan ba.

Lionel Messi ya zura kwallaye biyu a fafatawar ta jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.