Isa ga babban shafi
Wasanni-Ingila

An dakatar da Dan Evans daga kwallon Tennis na shekara guda

An dakatar da dan wasan tennis na Ingila Dan Evans daga buga wasanni har na tsawon shekara guda bayan wani gwaji daya tabbatar da dan wasan yayi amfani da Hodar Cocaine. Tun a ranar 24 ga Aprilun daya gabata yayin gasar Barcelona Open ne aka fara zargin Evans da amfani da Cocaine lamarin daya sa aka fara bincike kan sa, inda kuma a lokuta da dama dan wasan ya sha musantawa.

Hukumar kula da wasannin Tennis ta ITF ta ce kamata ya yi a dakatar da Dan Evans na tsawon shekaru 4 sabanin watanni 12.
Hukumar kula da wasannin Tennis ta ITF ta ce kamata ya yi a dakatar da Dan Evans na tsawon shekaru 4 sabanin watanni 12. Reuters
Talla

Yanzu haka dai ba za a sake ganin Fuskar Dan Evans mai shekaru 27 kuma lamba hudu a kwallon Tennis a filin wasa ba har zuwa ranar 24 ga Aprilun 2018.

A wasu jawaban bankwana da Evans ya mika ga masoyansa ya ce tabbas ya cancanci ya dawo fagen wasan.

Hukumar kula da wasannin Tennis ta duniya ITF, ta ce la’akari da girman haramcin amfani da Cocaine a wasan Tennis tun farko shekaru hudu ya kamata a yankewa Evans sabanin watanni 12 da aka yanke a yanzu

Haka zalika ta bukaci Evan ya biya tarar Yuro dubu dari da 4 tare da ajje duk wata kyauta daya samu da kuma matsayin daya kai daga ranar da aka fara zarginsa zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.