Isa ga babban shafi
wasanni

Messi na fuskantar barazanar zuwa gasar kwallon duniya

Kasar Argentina da gwarzon dan wasanta Lionel Messi na fuskantar gagarumar barazanar samun gurbi a gasar cin kofin duniya a Rasha. Argentina za ta rasa gurbin muddin ta sha kashi a hannun Ecuardo a karawarsu ta yau.

Lionel Messi na fuskantar barazanar zuwa Rasha don buga gasar cin kofin duniya a badi
Lionel Messi na fuskantar barazanar zuwa Rasha don buga gasar cin kofin duniya a badi REUTERS/Agustin Marcarian
Talla

Amma idan kasashen biyu suka yi canjaras a filin wasa na Quito, babban birnin Ecuardo, to hakkan na nufin cewa, Argentinan za ta dogara ne da sauran sakamakon wasannin da wasu kasashen za su yi, in da za ta gane ko za ta Rasha ko kuma a'a.

Sai dai idan Argentina ta samu maki uku a karawar ta yau, to za ta samu damar sake karawa da New Zealand, kuma ana ganin mawuyaci ne ta gaza doke New Zealand.

Samun nasara akan New Zealand zai kai Argentina Rasha a shekara mai zuwa.

Sai dai abin tambaya ana shi ne, ko Argentina za ta iya doke Ecuardo, lura da cewa, raban da ta samu nasara a kanta a waje tun shekarar 2001?

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.