Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Tottenham da Madrid sun rike juna a Bernabeu

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya yaba wa ‘yan wasan shi kan yadda suka yi kokarin rike Real Madrid kunnen doki a Santiago Bernabeu a fafatawar da suka yi jiya a gasar zakarun Turai.

Dan wasan Tottenham Harry Kane da Cristiano Ronaldo na Real Madrid
Dan wasan Tottenham Harry Kane da Cristiano Ronaldo na Real Madrid REUTERS
Talla

Tottenham ce ta fara cin Madrid kafin daga bisani Madrid ta rama kwallon.

Sakamakon dai ya yi wa Tottenham dadi domin tana kafada da Madrid da maki bakwai a rukuninsu na H.

Da Fanariti Cristiano Ronaldo ya rama wa Madrid kwallo a ragar Tottenham
Da Fanariti Cristiano Ronaldo ya rama wa Madrid kwallo a ragar Tottenham via Reuters/Andrew Couldridge

Hary Kane wanda tun kafin wasan Zidane ya jinjinawa, ya ce wasansu da Madrid ya nuna za su yi tasiri a gasar a bana.

Borussia Dortmund ta yi kunnen doki ne ci 1 da 1 a gidan APOEL Nicosia.

Tazarar maki 6 Madrid da Tottenham suka ba Dortmund kuma wannan babbar barazana ce ga kungiyar ta Jamus na yin ficewar gaggawa tun a zagayen farko a gasar.

Manchester City ke jagorantar rukunin F da maki 9 bayan ta doke Napoli ci 2-1.

Ana soma wasa da minti 9 Sterling ya fara ci wa City kwallo a ragar Napoli, sannan ana minti 13 Jesus ya ci kwallo ta biyu.

Kwallon da Gabriel Jesus ya ci a ragar Napoli
Kwallon da Gabriel Jesus ya ci a ragar Napoli via Reuters/Jason Cairnduff

Napoli ta samu jefa kwallo a ragar City a bugun fanariti da Diawara ya ci ana minti 73 da wasa.

Feyenoord ta sha kashi ne hannun Shakhtar Donetsk ci 2 da 1.

Livepool ta lallasa Maribor ne ci 7 da 0. Kwallaye biyu Firmino da Salah suka ci yayin da Coutinho da Chamberlin da Alexender-Arnold suka ci sauran kwallayen.

Kwallon da Roberto Firmino ya ci wa Liverpool a ragar Maribor
Kwallon da Roberto Firmino ya ci wa Liverpool a ragar Maribor REUTERS/Srdjan Zivulovic

Liverpool ce saman teburin rukuninsu na E da maki 5. Spartak Moscow ce ta biyu a rukunin ita ma da maki biyar bayan ta lallasa Sevilla 5 da 1.

Za a ci gaba da wasannin a Laraba

Benfica da Manchester United

CSKA Moscow da Basel

Bayern Munich da Celtic

Anderlecht da Paris Saint Germain

Qarabag da Atletico Madrid

Chelsea da Roma

Barcelona da Olympiakos

Juventus da Sporting Lisbon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.