rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Gasar Cin Kofin Duniya Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Putin ya gayyaci Blatter a gasar cin kofin duniya

media
shugaban Rasha Vladimir Putin ya gayyaci Joseph Blatter da Michel Platini a gasar cin kofin duniya a badi REUTERS/Ruben Sprich/Files TPX IMAGES OF THE DAY

Tsohon shugaban FIFA Sepp Blatter ya ce shugaban Rasha Vladimir Putin ya gayyace shi zuwa gasar cin kofin duniya da kasar za ta karbi bakunci a badi.


Blatter ya ce zai kalli wasannin duk da an haramta ma shi shiga harakar kwallon kafa.

Tsohon shugaban na FIFA ya fadi haka ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da kamfanin dillacin labaran Faransa AFP.

Kakakin gwamnatin Rasha Dmitri Peskov ya ce Putin zai ji dadin ganin Blatter a gasar domin abokan juna ne.

Haka kuma Blatter ya ce cikin wadanda Putin ya gayyata har da Michel Platini tsohon shugaban UEFA.

Kwamitin da’a na FIFA ne ya dakatar da Blatter da Platini na shekaru 6 daga shiga harakar kwallon kafa bayan badakalar rashawa ta kudi sama da dala miliyan biyu da ta shafe su.