Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal: Masu hannun jari sun ki amincewa da tazarcen shugabanni

Magoya bayan Arsenal, sun ki amincewa da sake zaben shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Chips Keswick, da kuma daraktan kungiyar Josh Kroenke, yayin taron da ya gudana a jiya Alhamis wanda ta saba yi a duk shekara.

Shugaban majalisar zartarwar Arsenal, Ivan Gazidis, yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Shugaban majalisar zartarwar Arsenal, Ivan Gazidis, yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters. REUTERS/Suzanne Plunkett/Files
Talla

Taron dai ya samu halartar magoya bayan na Arsenal 200 wadanda suka mallaki mafi tsokar hannun jari a kungiyar.

Yayin taron ne suka bukaci tilas shugabannin hukumar kungiyar su bada cikakken bayani kan dalilan da suka sanya su tsawaita yarjejeniyar shekaru biyu da mai horar da kungiyar ta Arsenal Arsene Wenger.

Zalika masu ruwa da tsakin sun kuma bukaci shugaban majalisar zartarwar kungiyar ta Arsenal Ivan Gazidis ya kare dalilin da yake dafe albashin Fan miliyan 2 da dubu dari 6 shi kadai, yayinda kuma yake karbe wani alawus din na fan miliyan daya daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.