rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Tseren Gudu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya: Mutane dubu 100 zasu fafata a tseren kilomita 10

media
Wasu 'yan Najeriya da suka fafata a gasar tseren gudun yada kanin wani karo na biyu da ta gudana a birnin Legas a kudancin Najeriya. BusinessDay

Sama mutane dubu 100 ne ake sa ran zasu shiga gasar tseren gudun yada kanin wani da bankin Access ke daukar nauyi a birnin Legas da ke kudancin Najeriya.


Shugaban tsara gasar Yusuf Ali ya ce babban burinsu shi ne sanya gasar tseren shiga tarihin da baza’a manta da shi ba a kundin hukumar lura da kuma shirya wasannin motsa jiki ta duniya.

A ranar 10 ga watan Fabarairu mai zuwa ne gagarumar gasar ta tseren gudun yada kanin wani zata gudana, kuma akalla shararrun maguda 200 zasu shiga wannan tsere.

A farkon shekarar 2017 da muke ciki mutane dubu 73,000 suka shiga gasar, abinda ya sa ta samu matsayin gasa ta 2 irinta mafi kayatuwa a nahiyar Afrika.

Wanda ya zo na daya zai lashe kyautar naira miliyan 3, da kuma sabuwar mota.