Isa ga babban shafi
Wasanni

Fasahar taimakawa alkalin wasa da bidiyo na fuskantar suka

Masu bibiyar wasannin kwallon kafa na gasar Bundisliga ta kasar Jamus, sun shiga sahun masu sukar amfani da maimaicin nuni na bidiyo don taimakawa alkalin wasa, inda suka bukaci hukumar kwallon kafa ta Jamus ta kawo karshen amfani da sabuwar fasahar da aka tsara don taimakawa alkalin wasa.

Fasahar amfani da bidiyo wajen taimakawa alkalin wasa.
Fasahar amfani da bidiyo wajen taimakawa alkalin wasa. FIFA.com
Talla

Masu bibiyar wasannin na Bundisliga sun bukaci haka ne bayanda suka zargi Hellmut Krug, shugaban sashin da ke lura da maimaita bidiyon wasannin a birnin Cologne da yin almundahana wajen tace wani yanki na bidiyon wasa don taimakawa kungiyar Schalke 04 da yake goyon baya, yayin wasan da aka tashi 1-1 tsakaninta da Wolfsburg.

Har yanzu dai sabon tsarin maimaita bidiyon wasannin yana matakin gwaji ne a kasashen Italiya da Jamus, kasancewar hukumar FIFA bata yanke shawara kan ko zata yi amfani da fasahar ba, wajen taimakawa alkalan wasa, yayin gasar cin kofin duniya da Rasha zata karbi bakunci a watan Yunin shekarar mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.