rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Olympic

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kwamitin IOC ya dakatar da wani kusa a cikinsa

media
Tsohon dan kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya IOC kuma tsohon dan wasannin motsa jiki mai wakiltar kasarsa ta Namibia. REUTERS/Scanpix/Keld Navntoft.

Tsohon dan tseren gudu na kasar Namibia,  Frankie Fredericks, ya rasa mukaminsa na mamba kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya IOC, bayaga mukamin da ya sauka daga kansa na dan majalisar zartaswa na hukumar shirya wasannin motsa jiki ta duniya IAAF.


Matakin ya biyo bayan samunsa da kwamitin na IOC yayi da aikata almundahanar karkatar da kudade da kuma karbar cin hanci, abinda kwamitin na IOC ya bayyana da cewa badakala ce da zata rage masa kima, yayin shirya wasannin na Olympics.

Masu gabatar da kara a Faransa, sun zargi Fredericks da laifin karbar cin hancin dala dubu 299,300 daga dan tsohon shugaban hukumar shirywa wasannin motsa jiki ta duniya IAAF Lamine Diack, a lokacin da birnin Rio na Brazil ya samu nasarar  karbar bakuncin gasar wasannin Olympics na shekarar da ta gabata 2016.

A zamanin da Fredericks ya fafata wasannin tseren gudu, ya lashewa kasarsa ta Namibia lambobin yabo har sau hudu, inda a gasar Olympics da aka yi a Barcelona, cikin shekarar 1992 ya lashe lambar azurfa a gasar tseren gudu na mita 100, da mita 200.

A gasar Olympics ta shekarar 1996 a Atlanta ma dai lambar Azurfan ya lashewa kasar tasa, sai kuma a ya lashe lambar Zinare a shekarar 1993, a tseren gudu na mita 100, yayin gasar wasannin motsa jiki ta duniya.