Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya nemi rabuwa da Madrid a karshen kaka

Rahotanni sun ce Cristiano Ronaldo ya ki amincewa da tayin rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar da kungiyarsa ta Real Madrid ta mika masa.

Shahararren dan wasan kwallon kafa na Real Madrid Cristiano Ronaldo.
Shahararren dan wasan kwallon kafa na Real Madrid Cristiano Ronaldo. REUTERS/Sergio Perez
Talla

A maimakon haka an rawaito cewa Ronaldo ya bayyana aniyarsa ta ficewa daga kungiyar ce a karshen kakar wasa ta bana.

Sai dai majiya mai tushe ta ce shugabannin kungiyar ta Madrid, sun yi watsi da bukatar Ronaldo, matakin da ya sake fusata dan wasan.

Tun da dadewa Ronaldo ya sha nanata cewa ba zai sabunta yarjejeniya da Madrid ba, wadda zata kare a shekarar 2021, zalika ko a kakar wasan da ta gabata, sai da Ronaldo ya yi barazanar raba gari da Madrid, musamman bayan zarginsa da rashin biyan haraji da hukumomin Spain suka yi, zargin da ya musanta.

Daga cikin kungiyoyin da zuwa yanzu, suka nuna muradin sayen Criatiano Ronaldo akwai, tsohuwar kungiyarsa Manchester United, Pari Saint Germain, Juventus, AC Milan, da kuma Inter Milan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.