Najeriya za ta yi wasanni da manyan kasashen duniya
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya Amaju Pinnick ya bayyana cewa, nan gaba tawagar Super Eagles za ta yi wasannin sada zumunta har guda biyar da manyan kasashen da suka yi fice a duniyar tamaula.
Wallafawa ranar:
Pinnick ya ce, suna shirin gudanar da wasannin ne gabanin gasar cin kofin kwallon duniya da Rasha za ta karbi bakwanci a badi.
Pinnick ya kara da cewa, sun mayar da mankali wajen ganin sun yi wasannin da kasashen da ke jan ragama a jadawalin Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya.
Sannan kuma kasashen su kasance cikin wadanda suka samu gurbi a gasar kofin duniya a Rasha.
Tuni dai Najeriya ta tuntubi wasu daga cikin kasashen don ganin cewa sun amince a yi wasannin na sada zumunta kafin zuwa Rasha a badi.
Sai dai kawo yanzu ba a bayyana sunayen kasashen ba, amma daga cikin ‘yan wasan na Najeriya akwai masu burin ganin cewa, sun yi wasa da Ingila.
Najeriya dai ta samu nasarar doke Argentina da ci 4-2 a wasan sada zumunta da suka yi a ranar 14 ga wannan wata na Nuwamba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu