rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Africa ta kudu Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotu ta kara wa'adin hukunci kan Pistorius

media
Oscar Pistorius REUTERS/Mike Hutchings/Files

Wata kotun daukaka kara a Afrika ta kudu ta kara wa’adin hukuncin daurin gidan yarin da aka yiwa zakaran wasan tseren nakasassu na Paralympic, Oscar Pistorius zuwa fiye da shekaru 13.


Matakin ya biyo bayan korafe-korafe kan hukuncin farko da Kotun ta yanke wa Pistorius na daurin shekaru shidda.

Duk da cewa Pistorius bai halarci zaman kotun na yau ba, amma alkalin da ya jagoranci zaman shari’ar ya zartas da hukuncin na daurin shekaru 13 da wata biyar kan kisan da ake zargin shi da yiwa budurwarsa Reeva Steenkamp.

Sai dai kuma wani babban jami’in shari’a Nazreen Shaik Peremanov ya ce, dan wasan na da ‘yancin daukaka kara a kotun kundin tsarin mulkin kasar.

Matakin kotun dai ya biyo bayan bukatar da masu shigar da kara suka shigar na cewa har yanzu Pistorius ya gaza gabatar da hujjoji kan zargin da ake masa.

Tun a ranar 14 ga watan Fabarairun shekarar 2013 ne Pistorius ya bude wuta kan budurwarsa Reeva, amma bayan wata shari’a a shekarar 2014 kotu ta sanar da cewa bata samu Pistorious da laifi ba bayan da ya yi ikirarin cewa lamarin ya faru ne bisa kuskure.

Sai dai kuma a shekarar 2014 kotu ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin zaman gidan maza yayin da aka fito da shi a shekarar 2015.