rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Rasha Olympic

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rasha ba za ta shiga gasar Olympic ta 2018 ba-IOC

media
Rasha ba za ta shiga gasar Olympic na 2018 ba inji IOC

Kwamitin shirya wasannin Olympic na duniya, IOC, ya haramtawa Rasha shiga gasar Olympic na shekara ta 2018, kan kwankwadan kwayoyin sa kuzari da 'yan wasanta ke yi.


Shugaban kwamitin, Thomas Bach, ya ce mu’amala da kwayoyin sa kuzari a wasa kalubaline ga martaban wasannin Olympic dama sauran wasanni baki daya.

Wannan haramci bai shafi ‘yan wasan Rasha da aka tabbatar ba sa shan kwayoyin sa kuzarin ba, sai dai ba za su yi amfani da tutar kasar ba, za su shiga gasar ne a matsayin masu zaman kansu karkashin inuwar tutar Olympic.

Kazalika an haramtawa Mataimakin Firaministan kasar Vitaly Mutko wanda tsohon ministan wasanni ne da mataimakinsa Yuri Nagornykh tsoma baki a harkan wasannin Olympic har karshan rayuwarsu.

Bayan Afirka ta kudu da aka haramtawa shiga gasar Olympic a lokacin wariyar launin fata, babu wata kasa da aka ta ba yi wa irin wannan haramcin sai Rasha.

Mista Mutko shi ne shugaban kwamitin shirya gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakwanci a shekara ta 2018.