Isa ga babban shafi
Wasanni

Kaka ya yi ritaya daga kwallon kafa

Tsohon dan wasan gaba na tawagar kwallon kafa ta kasar Brazil Ricardo Kaka, ya sanar da yin ritaya daga fagen kwallon kafa.

Tsohon dan wasan kungiyar AC Milan Ricardo Kaka yayin da yake murnar zura kwallo a ragar kungiyar Lazio, a wasan Serie A soccer da suka fafata a birnin Rome. 23 ga watan Maris, 2014.
Tsohon dan wasan kungiyar AC Milan Ricardo Kaka yayin da yake murnar zura kwallo a ragar kungiyar Lazio, a wasan Serie A soccer da suka fafata a birnin Rome. 23 ga watan Maris, 2014. REUTERS/Giampiero Sposito
Talla

Kaka mai shekaru 35, ya ce a halin yanzu, zai maida hankali ne, wajen ganin ana damawa da shi a fagen horarwa ko rike mukaman da suke da kusanci da hakan a kungiyoyi, a cewar shahararren dan wasan, tuni tsohuwar kungiyarsa ta AC Milan ta yi masa tayi.

Kaka ya fara wasa ne a kungiyar Sao Paulo da ke Brazil, inda shahararsa, ta ja hankalin manyan kungiyoyin nahiyar turai, hakan yayi sanadin komawarasa AC Milan a shekarar 2003.

A kungiyar ta Milan ce, Kaka ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya ta Ballon d’Or, kuma shi ne dan wasa na karshe da ya samu wannan kyauta, banda Cristiano Ronald da Lionell Messi da suka lashe ta hau sau biyar dukkaninsu.

A dai shekarar ta 2007 Kaka ya taimakawa AC Milan lashe kofin zakarun nahiyar turai karo na bakwai.

A shekarar 2009, Kaka ya koma kungiyar real Madrid kan kudi mafi tsada a waccan lokacin na euro miliyan 68. Sai dai sakamakon yawaitar fama da jin ciwo Kaka ya gaza haskawa a kungiyar, inda a shekarar 2003 ya sake komawa AC Milan, kafin daga bisani ya koma kungiyar Orlando City ta Amurka a 2014.

A jimlace Kaka a ci wa kasarsa ta Brazil kwallaye 29 daga cikin wasanni 92 da ya buga mata, yayin da a bangaren tsohuwar kungiyarsa da ya fi dadewa a cikinta kuwa, kwallaye 104 Kaka a ci wa AC Milan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.