Isa ga babban shafi
Wasanni

Harry Kane ya goge tarihin shekaru 22

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Harry Kane ya goge tarihin shekaru 22 da tsohon dan wasan Ingila Alan Shearer ya kafa a lokacin da ya buga wasannin Premier na Ingila.

Dan wasan gaba na kungiyar Tottenham Harry Kane.
Dan wasan gaba na kungiyar Tottenham Harry Kane. Paul Childs/Reuters
Talla

A lokacin da yake tare da Blackburn Rovers a shekarar 1995, Alan Shearer ya ci kwallaye 36 a kakar wasa guda, inda ya kafa tarihin zama dan wasan premier da ya fi cin kwallaye.

Sai dai a wasan da aka fafata dazu tsakanin Tottenahm da Southampton, Harry Kane ya ci kwallaye uku shi kadai inda suka lallasa Southampton da kwallaye 5-2.

Hakan ya bai wa Kane damar kai wa matakin Alan Shearer wajen shahara a kwarewar zura kwallaye.

Zalika Harry Kane ya zarta Lionel Messi wajen zama dan wasan da yafi kowa a nahiyar turai yawan kwallaye, sakamakon samun nasarar cin kwallaye uku a wasa guda, har sau shida a cikin kakar wasa ta bana kadai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.