Isa ga babban shafi
Wasanni

Madrid ta fi samun nasara a 2017 cikin shekaru 115 - Perez

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Florentino Perez, kamata ya yi daukacin magoya bayan kungiyar su yi tinkaho da nasarorin da ta samu a wannan shekara ta 2017.

'Yan wasan Real Madrid a lokacin da suke murnar lashe kofin gasar kungiyoyin kwallon kafa na Duniya, da aka fi sani da Club World Cup. Disamba, 16, 2017.
'Yan wasan Real Madrid a lokacin da suke murnar lashe kofin gasar kungiyoyin kwallon kafa na Duniya, da aka fi sani da Club World Cup. Disamba, 16, 2017. © REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Perez ya ce Madrid ta cancanci wannan goyon baya, duk da lallasa ta da Barcelona ta yi da kwallaye 3-0, a wasan La liga na el Classico da suka yi a ranar Lahadi da ta gabata, hakan yasa Barcelona ta bai wa Madrid din tazarar maki 14.

A kakar wasan da aka kammala cikin wannan shekarar ce, kungiyar Madrid ta kafa tarihin maimaita lashe, kofin gasar zakarun nahiyar turai a jere, da kuma lashe kofin gasar kungiyoyin kwallon kafa na duniya wato Club World Cup.

A dai wannan shekarar ta 2017 ce Real Madrid ta lashe Super Cup na Spain.

A cewar shugaban kungiyar Perez, wannan nasara ita ce mafi kayatarwa da girma a tsawon tarihin shekaru 115 na kafuwar Madrid.

Dangane da batun jita-jitar cewa kungiyar zata sallami kocinta Zinaden Zidan kuwa, Perez ya ce babu gaskiya bane, hasali ma su shugabanni suna tunkaho da Zidane din da kuma magoya bayansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.