Isa ga babban shafi
Wasanni

Benzema na fuskantar barazanar fara dumama benci a Madrid

Rahotanni daga Spain sun ce Mai horar da Real Madrid Zinaden Zidane ya amince da fara ajiye dan wasansa na gaba, Kareem Benzema a cikin ajin wadanda suke dumama benci.

Mai horar da kungiyar Real Madrid Zinaden Zidane tare da dan wasansa na gaba Kareem Benzema.
Mai horar da kungiyar Real Madrid Zinaden Zidane tare da dan wasansa na gaba Kareem Benzema. Eurosport
Talla

Matakin ya zo ne bayanda Benzema ya gaza tabuka abin azo a gani cikin wannan Kaka, inda ya zura kwallaye 2 kawai a wasannin La liga 12 da ya buga.

A cewar wata Majiya daga kungiyar ta Real Madrid, kafin zartas da matakin, Zidane zai bai wa Benzema damar buga wasanni biyu tsakanin Madrid da kungiyoyin Celta Vigo (a wasan Cope Del Rey), da kuma Villareal (a wasan La liga), muddin kuma ya gaza, to fa maida shi ajin 'yan dumama benci zai tabbata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.