rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Tennis

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Andy Murray ya dawo fagen wasan Tennis bayan fama da jinya

media
Har yanzu dai babu tabbacin ko Andy Murray zai fafata a gasar Australian Open da za a fara ranar 15 ga watan Janairun nan. Reuters/Toby Melville

Zakaran kwallon Tennis da ya sha fama da jinya tsawon lokaci Andy Murray ya ce akwai yiwuwar sauya salon wasansa sabanin yadda aka saba gani a baya.Kafin tafiyar jinyar zakaran kwallon na Tennis sai da ya sha fama da koma baya a harkokin wasansa.


A cewar tsohon kocin sa Miles Maclagan, Andy Murray mai shekaru 30 lamba 16 a fagen wasan Tennis na Duniya dole zai sauya salonsa sakamakon jinyar da ya yi fama da ita la’akari da cewa yanzu ba zai rika iya jure tsawon lokaci yana buga wasa ba.

A gasar Brisbane International ne dai Andy Murray ya sanar da cewar zai fice da ga gasar don duba lafiyarsa sakamakon raunin da ya samu a kwankwaso don yi masa tiyata.

Tsohon kocin na Murray wanda ya shafe fiye da shekaru uku yana kula da al’amuran wasansa ya ce kada masoya dan wasan su karaya domin nan gaba kadan zai kammala dawowa dai dai.

Murray dai ya sha fama da matsalar gaza yin doguwar tsayuwa a gasar Wimbledon lamarin da ya sa ya yanke hukuncin komawa ga likita don ayi masa tiyatar raunin da ya samu bayan shan kaye sau biyar a jere daga abokin adawarsa Sam Querrey cikin watan Yulin bara.

Sai dai kuma har yanzu babu tabbacin ko Andy Murray zai fafata a gasar Australian Open da za a fara ranar 15 ga watan nan ko akasin haka.