Isa ga babban shafi
Wasanni

Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na nahiyar Afrika

Muhammad Salah, ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafar nahiyar Afrika na shekarar 2017, abinda ya bashi damar zama dan wasan Masar na farko, da ya karbi wannan kyauta, tun bayan Mahmoud al Khatib a shekarar 1993, da kuma Mohammed Aboutrika a shekarar 2008.

Sabon gwarzon nahiyar Afrika, dan wasan kasar Masar Mohamed Salah, wanda ke bugawa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ke Ingila..
Sabon gwarzon nahiyar Afrika, dan wasan kasar Masar Mohamed Salah, wanda ke bugawa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ke Ingila.. REUTERS/Phil Noble
Talla

A ranar Alhamis ne a birnin Accra da ke Ghana, hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF ta karrama Salah, da ke bugawa kungiyar Liverpool wasa a ingila.

Salah mai shekaru 25, ya zura kwallaye 23 cikin dukkanin wasannin Premier 29 da ya buga a kakar wasa ta bana.

Zalika Muhammad Salah ya taimakawa Masar wajen samun tikitin halaratar gasar cin kofin duniya da za’a yi cikin wannan shekara a Rasha, karo na farko kenan da Masar ta samu irin wannan dama, tun bayan shekarar 1990.

Dan wasan na biyu da ke biye da Salah wajen kwarewa a zaben na hukumar CAF, shi ne Sadio Mane dan kasar Senegal, wanda shi ma ke bugawa kungiyar Liverpool wasa.

Sai kuma Pierre-Emeric Aubameyang dan kasar Gabon da ya zo na uku, wanda ke bugawa kungiyar Borussia Dortmund da ke kasar Jamus wasa.

Jami’an da suka gudanar da wannan zabe sun hada da masu horar kwallon kafa na kasashen nahiyar Afrika, jami’an hukumar kwallon kafar nahiyar CAF, ‘yan jaridu da kuma sauran mutane.

Sauran ‘yan wasa, tawagogin kwallon kafa da masu horarwa da suka zama gwarzayen Afrika na shekarar 2017 sun hada da, Azizat Oshoala ‘yar Najeriya da ta lashe kyautar gwarzuwar ‘yar kwallon Afrika ajin mata. Sai kuma matashin dan wasa mafi kwazo, Patson Daka dan kasar Zambia.

Hukumar CAF ta kuma zabi mai horar da tawagar kwallon kafa ta Masar, Hector Cupa, a matsayin gwarzo tsakanin takwarorinsa, zalika tawagar tasa da yake horarawa ta Masar, ta lashe kyautar mafi kwarewa ta kasashen nahiyar Afrika.

A bangaren tawagar kwallon kafar mata kuwa, kasar Afrika ta Kudu ce ta lashe wanna kyauta ta mafi kwarewa.

Sai kuma kungiyar kwallon kafa mafi kwazo da kwarewa, kyautar da kungiyar Wydad Casablanca ta kasar Morocco ta lashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.