rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Tennis

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rafael Nadal na samun gagarumar nasara a gasar Australian Open

media
Ficewar zaratan 'yan kwallon Tenis irinsu Andy Murray da Serena Williams daga gasar ta Australian Open ka iya bayar da dama ga Nadal ya kai kambunsa. REUTERS/Toby Melville

Dan wasan Tennis lamba daya a duniya Rafael Nadal dan Spain na ci gaba da samun jerin nasarori a gasar Australian Open da ke ci gaba da gudana inda ya yi nasara kan Damir zumhur lamba 26 na duniya dan Bosnia da ci 6 da 1, 6 da 3 da kuma 6 da 1 a zagaye da uku da fara wasa.


Nadal mai shekaru 31 sau daya rak ya taba lashe kyautar Australian Open cikin kyautukan Grand Slam 16 da ya taba lashewa.

Nadal zai kuma fafata da Marin Cilic a wasan na kusa dana kusa dana karshe kafin daga bisani ya fafata zagaye hudu da Grigor Dimitrov ya kuma yi wasan karshe da Roger Faderer, matakin da anan ne ake ganin zai iya fuskantar tangarda.

To gab da fara wannan gasa ne dai manyan zakarun wasan na Tennis irinsu Serena Williams da Andy Murray suka sanar da ficewarsu daga gasar ta Australian Open sakamakon rashin lafiya matakin da ake ganin a wannan karon zai iya taimakawa  Rafael Nadal ya kara rike kambunsa.