rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Tennis

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Djokovic na shan kaye a Australian Open

media
Ana dai alakanta, shan kayen na Djokovic a wanann karon da rashin murmurewa daga ciwon kafadar da ya yi fama da shi. Reuters/Matthew Childs

Tsohon lamba daya na duniya A wasan Tennis Novak Djokovic na ci gaba da shan kaye a gasar Australian Open bayan da dan wasan Korea ta kudu Hyeon Chung lamba 26 ya yi nasara akan sa har sau uku da ci 7-6, 7-5 da kuma 76.


Chung dai shi ne dan kasar Korea ta kudu da ya taba kai wa mataki na takwas din karshe don lashe kyautar Grand Slam.

Haka zalika shi ne dan wasa daya tilo da yanzu ke baiwa tsohon zakaran duniyar Novak Djokovic wahala a gasar ta Australian Open.

Ko da yake dai ana ganin nasarar Chung bata rasa nasaba da rashin kammala murmurewar tsohon zakaran duniyar Novak Djokovic sakamakon ciwon kafadar da sha fama da shi.

An dai fara gasar daga ranar 15 ga watan nan, wadda kuma za a karkare a ranar 28 ga wata.

Tun kafin fara gasar ta Australian Open zaratan 'yan wasan na Tennis irinsu Serena Williams da Andy Murray sun sanar da ficewarsu sakamakon rashin lafiya.