Isa ga babban shafi
Wasanni

Ingila: Kungiyoyi sun kashe Fam miliyan 430 wajen sayen 'yan wasa

Kididdiga ta nuna cewa kungiyoyin kwallon kafa da ke gasar Premier, sun kashe Fam miliyan 150 a ranar 31 ga watan Janairu, ranar karshe da aka ware cikin watan domin cinikin ‘yan wasa.

Hoton tamaula da ake shirin bugawa a gasar Premier, wasa tsakanin kungiyoyin Burnley da Everton a ranar 23 ga Agusta, 2009.
Hoton tamaula da ake shirin bugawa a gasar Premier, wasa tsakanin kungiyoyin Burnley da Everton a ranar 23 ga Agusta, 2009. REUTERS/Nigel Roddis
Talla

Hakan ke nuna a tsawon kwanaki 31 na watan Janairun da aka shafe kungiyoyin  sun kashe Fam miliyan 430 kenan wajen cinikin 'yan wasan.

Mafi tsadar cinikin da ya gudana a ranar karshe ta kasuwar ‘yan wasan shi ne sayen Pierre-Emerick Aubameyang da Arsenal ta yi daga Borussia Dortmund kan Fam miliyan 56.

Aubameyang ya bugawa Dortmund wasanni 213, ya ci kwallaye 141, zalika a wasanni 24 da ya bugawa Dortmund din cikin kakar wasa ta bana, ya ci kwallye 21 kafin komawa Arsenal.

Ita kuwa kungiyar Tottenham ta sayi Lucas Moura mai shekaru 25, na kungiyar PSG kuma dan kasar Brazil kan fam miliyan 23.

Lucas Mora ya bugawa PSG wasanni 229, ya ci kwallaye 46, ya kuma taimaka an zura kwallayen sau 50.

Dan wasan gaba na Arsenal Olivier Giroud, ya koma Chelsea kan fam miliyan 18, yayin da Andre Ayew dan kasar Ghana ya koma tsohuwar kungiyarsa Swansea daga West Ham shima akan fam miliyan 18.

Babban cinikin da bai yi nasara ba kuwa shi ne tsakanin Manchester City da Leicester City, kan dan wasan gaba na kungiyar ta Leicester, wato Riyad Maharez.

Cinikin ya rushe ne, bayan da Leicester City ta nemi Manchester City ta biya Fam miliyan 95 kan Maharez, bukatar da City ta yi watsi da ita, inda ta taya dan wasan kan fam miliyan 60.

A dai cikin watan Janairu Theo Walcott, ya koma kungiyar Everton daga Arsenal.

A shekarar 2006 Walcott ya koma Arsenal daga Southampton a lokacin da ayke da shekaru 16 kawai, ya shafe shekaru 12 a Arsenal, inda ya buga mata wasanni 397, ya kuma zura kwallaye 108.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.