rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Premier League

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zan kwatanta bajintar da Henry ya yi a Arsenal - Aubameyang

media
Sabon dan wasan gaba na Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang tare da mai horar da kungiyar Arsene Wenger. REUTERS

Sabon dan wasan gaba na kungiyar Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang, ya ce zai yi iyaka kokarinsa wajen kwatanta bajintar da tsohon dan wasan kungiyar Thierry Henry ya yi, a lokacin da ya ke bugawa kungiyar wasa.


Kafin komawarsa Arsenal, Aubameyang ya samu nasarar ci wa Borussia Dortmund kwallaye 98 a wasannin Bundesliga 141 da ya buga mata.

Dan wasan ya ce tabbas, bai kai matsayin da za’a daidaita shi da Henry ba, idan aka yi la’akari da cewa, tsohon dan wasan ya ci wa Arsenal kwallaye 228 a wasanni 377 da ya buga mata, amma zai gwada irin nasa kokarin don kamanta irin bajintar ta Thiery Henry.