rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa La liga

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Muna fuskantar kalubale a kakar wasa ta bana - Zidane

media
Mai horar da kungiyar Real Madrid Zinaden Zidane. Reuters/Juan Medina

Mai horar da Real Madrid Zinaden Zidane ya bayyana bacin ransa dangane da rashin samun nasarar da ‘yan wasansa suka yi, a fafatawarsu da kungiyar Levente.


Yayin wasan na La liga a ranar Asabar, Real Madrid tana gaf da samun nasarar doke Levente da kwallye 2-1, dan wasan Levente Giampaolo Pazzini ya rama kwallo ta biyu a minti na 89, inda suka tashi 2-2.

Real Madrid masu rike da kofin gasar ta La liga a yanzu suna matsayi na 4 a tsakanin kungiyoyi 20 da ke fafatawa a gasar, ya yin da kungiyar Barcelona da ke mataki na daya ta bata tazarar maki 18.

Karo na 6 kenan Madrid tana buga wasa canjaras ko kunnen doki a kakar wasa ta bana, inda kuma ta yi rashin nasara a wasanni 4.

Zidane ya koka bisa cewa kungiyarsa na fuskantar kalubalen da ta dade bata ga irinsa ba, kasancewar sun gaza samun nasarori a akalla wasanni 6 a jere.