rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tseren Gudu Wasanni Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Birtaniya za ta karbi bakoncin wasannin Athletics a bana

media
Kasashen da za su halarci gasar ta guje-guje da tsalle-tsallen a bana sun hadar da Birtaniya da Amurka da Poland da France da China da Jamus da Jamaica da kuma Afrika ta kudu. Reuters/路透社

Birtaniya za ta karbi bakonci gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Athletics a bana, gasar da manyan kasashen duniya 8 za su fafata.Kasashen da za su halarci gasar ta guje-guje da tsalle-tsallen a bana sun hadar da Birtaniya da Amurka da Poland da France da China da Jamus da Jamaica da kuma Afrika ta kudu.


Za a kaddamar da fara wasannin a ranakun 14 da 15 na watan Yuli rana guda da ranar da za a kammala gasar cin kofin duniya ta 2018 da za ta gudana a Rasha, haka zalika dai dai da ranar da za a kammala gasar Wibledon.

Dokokin gasar ya kunshi cewa dole ne a kowanne rukuni na wasannin asamu mace da namiji guda-guda da za su wakilci kasa.

Gasar wadda za a karkare a cikin kwanaki biyu kadai na karshen mako kasar da ta yi nasara za ta lashe kyautar kudi kusan Yuro milyan biyu baya ga sauran kyautuka.