rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kwamitin La Liga zai binciki Pique na Barcelona

media
Gerard Pique na fuskantar barazanar haramcin wasanni uku nan gaba REUTERS

Shugaban gasar La Liga ta Spain, Javier Tebas ya ce, hukumomin kwallon kafar kasar za su gudanar da bincike kan yadda dan wasan baya na Barcelona Gerard Pique ya nuna murnarsa ta barke kwallon da Espanyol da zura musu a karawar da suka yi a ranar Lahadi.


Pique wanda ya barke kwallon ana dad da tashi wasan, ya sanya dan yatsarsa akan lebensa da nufin magoya bayan Espanyol su yi tsit da bakinsu, lamarin da ya harzuka magoyan bayan har suka mayar da zazzafan martani.

Matukar dai kwamitin gasar La Liga ya samu Pique da laifi, akwai yiwuwar haramta ma sa wasanni uku nan gaba.

Pique ya yi kaurin suna wajen nuna adawarsa da magoya bayan Espanyol, in da kuma yake yawan yaba musu magana, yayin da ya zargi magoya bayan da zagin iyalansa.