rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Leceister City za ta maye gurbin Mahrez da Hazard

media
Riyad Mahrez na bakin-cikin rashin zuwa Manchester City daga Leceister City dailymail

Rahotanni na cewa, Leicester City na duba yiwuwar sauya dan wasanta na gaba Riyad Mahrez da dan uwan Eden Hazard, wato Thorgan Hazard da ke taka leda da Borussia Monchengladbach a Jamus.


A watan jiya ne aka bukaci Mahrez da ya jajirce don ganin ya koma Manchester City da taka leda amma Leiceter City ta dage kan cewa, ba za ta sallama dan wasan ba akan farashin da ya yi kasa da Pam miliyan 90.

Tun daga wannan lokacin, Mahrez dan asalin Algeria ke kaurace wa atisaye tare da kungiyar don nuna bakin-cikinsa akan abin da ta yi ma sa na hana shi zuwa Manchester City.

Tuni dai mahukuntan kungiyar suka fara nazarin maye gurbin Mahrez da kwararren dan wasa kuma ana kyautata zaton Thorgan Hazard za ta dauko.