rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Watford ta lallasa Chelsea da ci 4-1

media
Eden Hazard na Chelsa na cikin damuwa bayan Watford ta lallasa su REUTERS/David Klein

Kungiyar kwallon kafa ta Watford ta lallasa Chelsea da ci 4-1 a fafatawar da suka yi ajiya a gasar Premier ta Ingila.


Watford ta samu gagarumar nasarar ce bayan ta zura kwallaye uku ana dab da tashi wasan, kuma a karon farko kenan da ta ke samun nasara a gida a karkashin kocinta Javi Gracia, yayin da takawaransa na Chelsea, Antonio Conte ke dada fuskantar matsin lamba, bayan Chelsea ta sha kashi karo na biyu a jere a gasar Premier.

Antonio Conte ya ce, ya dace kungiyar ta dauki wani mataki matukar tana ganin ba ta gamsu da irin rawar da ya yake takawa ba a yanzu.

Chelsea wadda ke rike da kambi ta yi wasan ne da Olivier Giroud da ta dauko daga Arsenal gabanin rufe kasuwar cinikayyar ‘yan wasa a watan Janairu, kuma a karon farko kenan da ya fara taka ma ta leda.

Yanzu haka Watford na saman matakin rukunin ‘yan dagaji da maki 6 wanda ta samu daga wasanni 12 da ta yi buga.