rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Ingila Spain

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Chelsea ta fara zawarcin Marco Asensio

media
Matashin dan wasan kungiyar Real Madrid Marco Asensio. Reuters/Susana Vera

Kungiyar Chelsea ta fara zawarcin dan wasan Real Madrid Marco Asensio a matsayin bangaren yarjejeniyar da take son cimma tsakaninta da Real Madrid, dangane da saida wa Madrid din dan wasanta na gaba Eden Hazard.


Jaridar labaran wasanni ta Don Balón da ake wallafa ta a Spain ta rawaito cewa Chelsea na kokarin tsohe Baraka ko gazawar da zata samu ne, muddin Hazard ya sauya sheka zuwa Madrid.

Sai dai jaridar ta Don Balon ta rawaito cewa kungiyar ta Chelsea ta ce a shirye ta ke ta sayi Asensio, ko da kuwa dan wasanta Hazard ya zabi ci gaba da zama a cikinta.

Chelsea ta amince da biyan Fam miliyan 119 domin sayan Marco Asensio mai shekaru 22.