rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Premier League La liga

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Akwai yiwuwar na koma Real Madrid - Morata

media
Dan wasan gaba na kungiyar Chelsea Alvaro Morata yayin da yake murnar zura kwallo a ragar kungiyar Stoke City. REUTERS/Andrew Yates

Dan wasan gaba na Chelsea, Alvaro Morata ya ce mai yi wuwa ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Real Madrid.


Dan wasan dai bai wuce kai shekara guda da komawa Chelsea daga Madrid ba, wannan rahoto ya bulla, da ke tabbatar da cewa, Morata ya bayyana sha’awar ta sa.

Morata mai shekaru 25, da Chelsea ta saye shi daga Madrid kan kudi Fam miliyan 60 a watan Yulin shekarar da ta gabata, ya ci wa kungiyar kwallaye 10 a kakar wasa ta bana.

A halin yanzu Morata yana fama da ciwo a bayan sa, zuwa yanzu kuma babu tabbacin ranar da zai dawo filin wasa, kamar yadda mai horar da shi Antonio Conte ya tabbatar.