rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Manchester ba za ta iya doke Newcastle ba-Mourinho

media
Kocin Manchester United, Jose Mourinho Reuters/Carl Recine

Mai horar da Manchester United, Jose Mourinho ya ce, ko da kungiyarsa za ta shafe tsawon sa’oi 10 tana fafatawa da Newcastle, ba za ta zura kwallo guda ba a St James Park.


Mourinho ya bayyana haka ne bayan Manchester United ta sha kashi da ci daya mai ban haushi a karawar da ta yi da Newcastle a jiya a gasar firimiya ta Ingila.

Mourinho ya ce, ‘yan wasan Newcastle sun zage dantse sosai wajen ganin sun samu maki, yayin da yace, abin da suka yi yana da kyau muddin suna muradin lashe karawar.

Sai dai ya kara da cewa, ‘yan wasan na Newcastle sun yi wasan na jiya ne tamkar dabbobi don ganin sun samu nasara a gida kuma a karon farko tun cikin watan Oktoba a gasar ta firimiya a Ingila.

Yanzu haka sau biyar kenan Manchester United ke shan kashi a gasar  ta bana, in da kuma Newcastle ta fitar da kanta daga matakin ‘yan dagaji sakamakon kwallon da Matt Ritchie ya ci ma ta a jiya.

Ita ma Liverpool ta samu nasara a kan Southampton da ci 2-0 a fafatawar da suka yi a gasar  a jiya, yayin da Huddersfield ta lallasa Bournemouth da ci 4-0.