rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Conte ya samu goyon bayan 'yan Chelsea

media
Antonio Conte ya lashe kofin firimiya a bara Action Images via Reuters/John Sibley Livepic

Kocin Chelsea, Antonio Conte ya jinjina wa magoya bayan kungiyar kan yadda suka mara ma sa baya bayan nasarar da ya samu ta casa West Brom da ci 3-0 a Stamford Bridge a gasar firimiya ta Ingila.


Magoya bayan na Chelsea sun yi ta rere waka da sunan Conte, abin da ke nuna cewa, suna tare da shi.

Wannan nasarar ta rage matsin lambar da Conte ke fuskanta, in da har aka fara nazari game da makomarsa a kungiyar bayan ya gaza samun nasara a Bournmouth da Watford.

Yanzu haka Chelsea mai rike da kambi ta koma mataki na hudu a teburin gasar firimiyar, yayin da Conte ya ce, ya zama dole ya mika godiyarsa ga magoya bayan Chelsea.