rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ryan Mason ya yi ritayar dole daga kwallon kafa

media
Tuni dai dai-daikun ‘yan kwallo da kuma kungiyoyi ciki har da Chelsea wadda yayin wasansu da ita ne Mason ya gamu da ciwon suka fara mika sakon fatan alkhairi da kuma alhinin rashin fitaccen dan wasan a fagen tamaula. REUTERS

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Hull City Ryan Mason ya mika takaddar ritayarsa bisa tilasci ga hukumar gudanarwar Club din sakamakon cutar da ya ke fama da ita.


Mason dan birtaniya mai shekaru 26 likitoci a birnin London sun gargade shi ga yiwuwar salwantar rayuwarsa matukar ya kafe wajen ci gaba da doka tamaula.

Tun a bara ne Mason ya samu karaya a kokon kanshi bayan wata buguwa da ya yi da Gary Cahill na Chelsea lamarin da ya kwantar da shi har jinyar watanni 12.

A watan Agustan shekarar 2016 ne Mason ya koma Hull City daga Tottenham kan Yuro miliyan 13

Bayan shafe tsawon lokaci yana jinya a watan mayun bara ne Mason ya koma atisaye da Club din amma kuma ba tare da ya fara shiga wasanni ba.

Cikin takaddar ritayar ta Mason da ya mika a yau, ya yaba da dukkanin kokarin da Clun din ya yi masa haka zalika ya yabawa magoya bayansa.

A bangare guda shima Club din ya yi masa fatan alkhairi ga rayuwarshi ta gaba.

Tuni dai dai-daikun ‘yan kwallo da kuma kungiyoyi ciki har da Chelsea wadda yayin wasansu da ita ne Mason ya gamu da ciwon suka fara mika sakon fatan alkhairi da kuma alhinin rashin fitaccen dan wasan a fagen tamaula.