rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yau za a ci gaba da gasar zakarun Turai

media
An koma gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai REUTERS/Jean Pierre Amet

A yau za a ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, matakin kungiyoyi 16 da suka saura, in da FC Basel za ta kara da Manchester City.


To akwai yiwuwar dan wasan Manchester City Leroy Sane ya buga wasan na yau bayan raunin da ya samu a wasan da kungiyarsa ta lashe kofin FA a Cardiff a ranar 28 ga watan Janairu, in da aka za ci zai yi jinyar makwanni 6.

Sai dai kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce, dan wasan mai shekaru 22 ya koma taka leda duk dai bai kammala murmurewa yadda ya kamata ba.

Guradiola ya ce, dan wasan ya nuna sha’awar taimaka wa Manchester City.

To a bangaren Basel kuwa, David Silva da Fabian Delph duk za su fafata a wasan na yau bayan sun yi fama da rauni a kwankwaso da gwiwa.

A karon farko kenan da za a yi karan batta tsakanin Manchester City da Basel.

Ita ma dai Juventus za ta kece raini da Tottenham a filin wasa na Allianz a gasar ta zakarun na Turai.

Dan wasan baya na Tottenham, Toby Alderweired ba zai samu damar buga wasan na yau ba sakamakon raunin da ya samu tun a cikin watan Nuwamban bara, sannan kuma ba ya cikin tawagar Tottenham da ta doke Arsenal a ranar Asabar.

Hakan ma Juan Foyth da Kyle Walker-Peters duk ba za su samu damar buga wa Tottenham wasan na yau ba.

A bangaren Juventus kuwa, ‘yan wasanta Paulo Dybala da Juan Cuardrado da Andrea Barzagli da Blasie Matuidi duk ba za su buga wa kungiyar ba.