rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Neymar zai yi gaba da gaba da Ronaldo

media
Neymar da Lionel Messi da kuma Cristiano Ronaldo FABRICE COFFRINI / AFP

Dan wasa mafi tsada a duniya wato Neymar na PSG zai yi gaba da gaba da gwarzon dan kwallon duniya na Real Madrid wato Christiano Ronaldo a wasan da kungiyoyin biyu za su yi a yau a gasar zakrun nahiyar Turai


Madrid za ta yi wasan na yau ne a dai dai lokacin da kocinta Zinedine Zidane ke shan matsin lamba duk dai ya ce, ba zai bari wani abu ya daga ma sa hankali ba domin ya mayar da hankalinsa kacokan kan wasan na yau.

A bara dai Madrid ta kafa tarihi na kare kanbinta a gasar ta zakarun Turai tare kuma da lashe kofin La Liga a karon farko tun shekarar 2012.

Sai dai a bana, tuni aka yi waje da Real Madrid daga gasar Copa del Rey, in da kuma ta ke mataki na hudu a teburin gasar La Liga bayan Barcelona mai jan ragamar teburin ta ba ta tazarar maki 17.

Ita ma Liverpool za ta kece raini da FC Porto a yau a gasar ta zakarun nahiyar Turai.